Ganuwar Kano: Fitaccen ginin tarihi da ake shirin dawo masa da kimarsa

Kano city wall 750x430
Kano city wall 750x430

Birnin Kano, wanda ke arewacin Nijeriya, nan ne mahaifar wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Aliko Dangote haka kuma nan ne mahaifar tsofaffin shugabannin Nijeriya biyu, Murtala Muhammad da Sani Abacha.

Sai dai tarihi ya dora Kano a can sama ta bangaren ci-gaba idan aka kwatanta ta da sauran manyan birane na nahiyar.

Tun bayan da aka kafa birnin a karni na goma, ya yi fice ta bangaren kasuwanci da diflomasiyya da siyasa da kuma tashi da saukar jirgin sama.

Sarakai masu karfin iko da dama sun mulki Kano har zuwa lokacin da Birtaniya ta ci birnin da yaki a 1903 karkashin jagorancin dakarun Lord Lugard.

Duk da cewa ta lalace, amma ganin cewa ta shafe akalla karni takwas ya sa masana tarihi ke kallon ganuwar Kano a matsayin mafi dadewa a nahiyar Afirka. Ganuwa irin ta Kano da ke a birane da dama ko dai an sauya musu wuri ko kuma an lalata su a tsawon shekarun da suka gabata.

Bangon da ya zagaye birnin wanda aka fi saninsa da Ganuwa ko Garu ko kuma Badala, a gina shi ne da tubali kuma shi ne ya zagaye tsohon birnin na Kano.

Abin mamaki ne a yi tunanin wannan ganuwar ta kasance zagaye da birnin na kusan shekara 1,000.

Dakta Mahmud Abba, mai bincike kan birane na zamani da kuma na dauri masu ganuwa, da kuma abokin aikinsa Dakta Murtala Uba Mohammed na Tsangayar Nazarin Kasa da Muhalli a Jami’ar Bayero da ke Kano na kallon Ganuwar Kano a matsayin wadda ta wuce yadda ake tunani.

Kamar yadda suka bayyana, tsohon birnin ya kasance wata cibiyar kasuwanci wadda ke dauke da kasuwanni mafi dadewa a Afirka, wadanda suka hada da kasuwar Kurmi da ta shafe shekara 1,000 inda ‘yan kasuwa ke zuwa daga yankin Bahar Rum domin kasuwancin kayayyaki da suka hada da kayan kanshi da fata da tufafi da karfe da dai sauransu.

Yadda Kano ta samu ci-gaba ta bangaren kasuwanci da masana’antunta na sarrafa auduga ya samu bunkasa ne sakamakon yadda jama’ar birnin ke da yawa da kuma son ci-gaba, kamar yadda masana biyun suka shaida wa TRT Afrika

Kano a matsayinsa na birni, na zagaye da manyan birane masu karfi. Wadanda suka yi fice a cikinsu sun hada da Zamfara da Kwararrafa da Katsina da Zazzau da Kanem Bornu da Songhai.

Baya ga dakaru da wadannnan birane suke da su, akwai wasu dakarun da aka kora da barayi da masu cinikin bayi duka wadanda suke shawagi cikin sahara da gefen birnin.

Domin bayar da kariya ga jama’ar birnin da ke kara yawa da kuma lura da shige da ficen jama’a Sarkin Kano na uku, Sarki Gijimasu, wanda ya yi sarauta tsakanin 1095 zuwa 1134, shi ya aza tubalin ginin ganuwar Kano.

Masu aikin gini da leburori ne suka yi ta yin ginin ganuwar karkashin jagoranci ko sa ido na wakilan sarki.

An yi ginin ganuwar ne da tubali na gargajiya wanda aka yi da bulo na kasa da busashiyar ciyawa. Sa’annan aka yi wa ganuwar yabe da makuba. Bayan haka sai aka yi wa ganuwar kofofi inda kowace kofa tana da sunanta na kanta.

Akwai masu gadi da ke kula da budewa da kuma rufe kofofin. Dole ne mutanen da ke zuwa birnin da daddare bayan an kulle kofofin ganuwar su jira a waje zuwa wayewar gari kafin a bude kofar.

A lokacin da ake gini da kuma bayan kammala ginin ganuwar, sarki da kansa a wasu lokuta yake zagaye domin ya duba ingancin ganuwar da kuma bayar da umarnin yi mata gyara idan tana bukata.

Dakta Mohammed na daga cikin wadanda suke da ra’ayin cewa alkinta ganuwar Kano ba wai ci-gaba ne ta fannin tarihi ba kadai har ma ga muhalli.

“Tsawon lokaci, ramukan da aka yi da daruruwan kududdufan da aka tona a lokacin ginin ganuwar sun kasance wata hanya ta ajiyar ruwa domin wanki da girki da abinci ga dabbobi.

Suna zama wurin tara ruwa da kuma zuke shi wanda hakan yana rage yiwuwar samun ambaliyar ruwa,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Dakta Mohammed na daga cikin masu kira da a yi amfani da hanyoyi mafi kyau na kasa da kasa domin alkinta kayayyakin tarihi na Kano.

“Wannan ce hanyar da ‘ya’yanmu da jikoki za su girmama jini da zufar kakaninmu, wadanda suka kare Kano da kuma mika mana ita,” in ji shi.

Ganuwar Kano wadda ta zagaye birnin kuma ta sha gwagwarmaya da sauyin yanayi da na matsalolin muhalli iri daban-daban, ganuwar dai ta bace a sassa daban-daban na birnin a wasu wuraren kuma ta lalace inda take bukatar gyara.

Kofofin ganuwar ne kadai suke tsaye da kafafuwansu, su ma sakamakon yadda aka gyara su ba yadda suke a gargajiyance ba. Sauran ko dai sun bace ko kuma sun buya a cikin sabbin gine-ginen zamani da aka yi.

Dakta Mahmud ya koka kan yadda aka mayar da ganuwar ta Kano filayen sayarwa haka kuma ganuwar ba ta kasance daya daga cikin wuraren tarihi da hukumar al’adu da kimiyya ta Majalisar Dinkin Duniya ta san da zamansu ba.

Nasiru Wada Khalil, wani mai son raya al’adu ne, kuma ya ce idan har kasashe kamar India za su iya alkinta wuraren tarihinsu kamar Taj Mahal wanda bai kai shekara 500 ba, da kuma samar da wurin zuwa yawon bude ido “bai kamata mu rasa ganuwar Kano da ta shafe shekara dubu ba”.

“Ganuwar Kano a duka girmanta ita ce abin da za mu nuna wa ‘ya’yanmu da kuma baki da masu yawon bude ido, a matsayin abin tarihinmu da kuma wani matakinmu na ci-gaba,” in ji shi.

Dakta Mahmud ya nuna rashin jin dadinsa kan cewa duk da kiraye-kirayen da aka rinka yi na mayar da ganuwar ta Kano yadda take amma an bari ta lalace. Sai dai a ‘yan kwanakin nan gwamnatin Kano ta sanar da shirinta na kara farfado da ganuwar ta Kano.

(TRT Afrika )

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here