Dattijon ƙasa Tanko Yakasai ya cika shekara 100, ya gudanar da taron addu’o’i na musamman

Tanko Yakasai 608x430

Dattijon ƙasa kuma shahararren ɗan siyasa Tanko Yakasai ya gudanar da taron addu’o’i na musamman a gidansa da ke Kano domin murnar cika shekara Ɗari a duniya, inda ya nuna godiya ga Allah, iyalansa da al’ummar Kano bisa yadda suka taru domin taya shi murnar wannan rana.

A yayin taron a ranar Juma’a, Yakasai ya bayyana farin cikinsa a kan yadda dangi, abokai da abokan siyasa suka taru domin nuna goyon baya da kauna, tare da jin daɗin wannan babban lokaci na rayuwarsa.

Ya bayyana cika shekaru Ɗari a matsayin wata ni’ima ta musamman, tare da gode wa Allah bisa tsawon rayuwa da ya ba shi har zuwa wannan lokaci mai muhimmanci.

Dattijon ya yi addu’a ga jihar Kano da ƙasar Najeriya gabaɗaya domin samun zaman lafiya mai ɗorewa, tare da jaddada bukatar shugabanni a kowane mataki su fifita haɗin kai, adalci da walwalar jama’a.

Har ila yau, ya yi fatan Allah ya ba duk mahalarta taron samar komawa gida lafiya, tare da yaba wa masu shirya taron bisa gudummawar da suka bayar wajen tabbatar da nasarar wannan biki.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya bayyana Yakasai a matsayin ɗaya daga cikin fitattun shugabannin siyasa na Najeriya, wanda ya bayar da gudummawa sosai ga ci gaban ƙasa tun farkon zamanin jamhuriya, tare da taka rawa wajen ba da shawara ga gwamnatoci daban-daban.

’Ya’yansa, ’yan uwa da abokan siyasa sun bayyana shi a matsayin madubin hikima, mutum mai sauƙi da kishin adalci, wanda ya yi tasiri a kan rayuwar al’umma da dama a fadin ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here