Ƴan sanda sun kama tsohon shugaban hukumar karɓar ƙorafi da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a ranar Juma’a.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa jami’an ’yan sanda sun iso cikin manyan motocin aiki tare da makamai, cikin yanayin firgitarwa, suna yi wa duk wanda ya yi yunƙurin tsoma baki barazanar harbi.
Wani ganau ya shaida wa jaridar Solacebase cewa an kama Rimin Gado ne a dandalin sa na lauyoyi da ke kan titin Zariya, inda ya nemi jami’an da su nuna masa takardar umarnin kamawa ko bayanin dalilin cafke shi, amma suka ƙi yin hakan.
Rahotanni sun ce jami’an sun sanar da cewa sun fito ne daga babban ofishin rundunar ’yan sanda ta ƙasa da ke Abuja domin gudanar da aikin.
Lauyansa, Abubakar Ridwan Zakariyya, ya bayyana cewa jami’an sun yi yunkurin kwace wayarsa tare da yi masa barazanar harbi yayin da ake cikin tashin hankali.
A gefe guda, kakakin rundunar ’yan sandan Kano, CSP Abdullahi Kiyawa, ya ce a ba rundunar lokaci domin tantance sahihancin bayanan da suka shafi kamun.












































