Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya yaba da kokarin shugaban kasa Bola Tinubu wajen inganta tattalin arzikin Najeriya da kuma karfafa zaman lafiyar kasa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Gowon ya bayyana hakan ne bayan wata ganawar sirri da ya yi da shugaban kasa a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda ya bukaci ‘yan Najeriya su marawa kokarin gwamnati baya wajen magance manyan kalubalen da kasa ke fuskanta.
Gowon ya bayyana cewa ziyarar tasa ta ba shi damar tattauna halin da kasa ke ciki da kuma musayar ra’ayoyi kan ci gaban kasa.
Ya kara da cewa tattaunawar da suka yi ta fi mayar da hankali kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya da sauran sauye-sauyen da ake samu a sassa daban-daban karkashin gwamnatin yanzu.
Ya bayyana cewa sun yi nazari kan ayyukan da shugaban kasa ke yi da kuma irin ci gaban da ake samu a Najeriya a bangaren tattalin arziki da sauran fannoni.
Gowon ya kuma bayyana cewa gwamnatin na kokarin magance matsaloli da dama da suka shafi bangarorin siyasa, tattalin arziki da zamantakewar al’umma a kasar.
Ya kara da cewa jagorantar kasa mai bambancin kabila da addini kamar Najeriya na bukatar a daidaita abubuwa da dama tare da ci gaba da kokari domin bunkasa ci gaban kasa.
Tsohon shugaban kasar ya amince cewa matsalar rashin tsaro na daga cikin manyan kalubalen da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.
Ya jaddada cewa shugaban kasa dole ne ya kula da fifikon kasa tare da kare muradun Najeriya da kuma hadin kan al’ummarta.
Gowon ya kuma bayyana cewa magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta babban nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati da hukumomin tsaro.
Ya nuna kwarin gwiwa cewa gwamnati da hukumomin tsaro na tafiyar da matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin Najeriya.
Ya bayyana fatan cewa kokarin da ake yi a halin yanzu zai kai ga dawo da cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.













































