Tashin hankali a Zamfara: An kashe Daraktan Kwaleji bayan ya biyan Naira Miliyan 25.7 da babura don ceto iyali daga hannun ‘yan bindiga

WhatsApp Image 2026 03 14 at 14.21.43 1 750x430

Kisan Malam Bashir Sani, babban jami’in gudanarwa a Kwalejin Ilimi ta Maru da ke Maru a Jihar Zamfara, da ake zargin ‘yan bindiga ne suka aikata, ya sake bayyana mummunan halin rashin tsaro a wasu sassan arewacin Najeriya, inda iyalai da ke biyan kudin fansa domin kubutar da ‘yan uwansu ke ci gaba da fadawa cikin jerin sace-sacen mutane.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa marigayi Bashir Sani ya taba biyan akalla Naira Miliyan 25.7 a matsayin kudin fansa da sauran bukatun da ‘yan bindiga suka nema a tsawon shekaru domin kubutar da wasu ‘yan uwansa da aka sace kafin daga bisani shi ma aka kashe shi.

‘Yan uwa da majiyoyin al’umma sun bayyana cewa hare-haren da ake kai wa iyalan sun fara ne shekaru da suka wuce lokacin da ‘yan bindiga suka sace matansa biyu daga gidansu da ke Tsohon Tasha a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Domin kubutar da su, an biya Naira Miliyan biyu ga masu garkuwar.

Bayan wasu watanni, ‘yan bindigar sun sake dawowa inda suka sace kanensa mai suna Hassan Sani, lamarin da ya tilasta wa iyalin sake shiga tattaunawa da masu garkuwar.

Hassan Sani ya bayyana cewa dan uwansa ya biya Naira Miliyan 3.5 domin kubutar da shi, baya ga katin caji da wayoyin hannu da ‘yan bindigar suka bukata kuma aka kai musu.

Yawan hare-haren ya jefa iyalin cikin fargaba, wanda hakan ya sa Malam Bashir Sani ya sauya matsuguni tare da iyalansa zuwa wani wuri mai yawan jama’a a cikin garin Maru domin neman kariya.

Bayan kusan watanni 18 da suka samu kwanciyar hankali, ‘yan bindigar sun gano sabon wurin da suke zaune suka sake kai hari, inda suka sace Malam Bashir Sani da daya daga cikin matansa da aka taba sacewa a baya da kuma ‘yarsa tare da wasu mazauna unguwar.

A harin kuma, an kashe matar wani dan sanda tare da sace ‘ya’yanta biyar, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.

‘Yan bindigar sun bukaci a biya Naira Miliyan 20 domin sakin Bashir Sani da ‘yan uwansa.

Iyalan sun ce daga karshe an biya kudin fansar gaba daya, baya ga babura, katin caji na Naira Dubu Ɗari Biyu da kuma wayoyin hannu guda hudu da aka kai musu.

Duk da haka, ‘yan bindigar sun ci gaba da kara bukatunsu, inda daga baya suka nemi babura 15, amma bayan tattaunawa aka rage zuwa babura uku da iyalan suka saya suka kai musu.

Bayan an kai baburan, ‘yan bindigar sun bukaci iyalan su koma gida su jira karin bayani kan sakin wadanda aka sace.

Sai dai daga baya aka gano cewa a lokacin da ake tattaunawar, tuni Malam Bashir Sani ya rasu a hannunsu.

Daga bisani, masu garkuwar sun umarci iyalan su je kauyen Gidan Kano da ke karamar hukumar Maradun domin karbar ‘yan uwansu da aka sako.

Da suka isa wurin, sun samu matarsa da ‘yarsa da sauran wadanda aka sako, amma Bashir Sani bai kasance tare da su ba.

Matarsa ta bayyana cewa ya rasu ne yayin da yake tsare a sansanin ‘yan bindigar bayan ya sha wahala da kuma fama da matsalolin lafiya, ciki har da karyewar kafa da ba a kula da ita ba.

Mazauna Maru sun bayyana lamarin a matsayin wani abin tausayi da ke nuna irin matsalar rashin tsaro da ke addabar al’ummomin karkara a jihar Zamfara, inda kungiyoyin ‘yan bindiga ke ci gaba da sace mutane domin neman kudin fansa.

Shugabannin al’umma sun ce marigayi Bashir Sani mutum ne da ake girmamawa sosai a matsayin malami da jami’in gudanarwa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar jama’a da kuma bunkasa ilimi a yankin.

Mutuwarsa ta sake tayar da kira ga gwamnati da ta dauki matakai masu karfi domin inganta tsaro da kare al’ummomin da ke cikin hadari a jihar Zamfara da sauran sassan arewacin Najeriya da ke fama da matsalar ‘yan bindiga.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here