Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da rushe Ma’aikatar kula da manyan makarantu ta jihar Kano nan take, a wani mataki da gwamnati ta ce an dauka domin karfafa daidaiton aiki da kuma hanzarta sauye-sauye a bangaren ilimi na jihar.
Biyo bayan rushewar ma’aikatar, mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda kuma yake rike da mukamin kwamishinan kula da manyan makarantu, an sauke shi daga wannan karin mukami.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnatin ta bayyana cewa ayyukan da ma’aikatar da aka rushe take gudanarwa za a hada su karkashin wata hukuma guda.
Sanarwar ta ce sabon tsarin zai kasance karkashin Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, inda za a kafa wani sashe na musamman na kula da manyan makarantu a cikin ma’aikatar domin sa ido kan harkokin manyan makarantu.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wannan sashe zai kasance karkashin jagorancin babban sakatare tare da sauran ma’aikata domin tabbatar da ingantaccen gudanarwa da sa ido kan cibiyoyin manyan makarantu na jihar.
Sanarwar ta kara da cewa a karkashin sabon tsarin, dukkan hukumomin da ke karkashin tsohuwar ma’aikatar kula da manyan makarantu, ciki har da Hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Kano, za su koma karkashin ma’aikatar ilimi, yayin da jami’o’in da jihar ke da su da sauran cibiyoyin manyan makarantu za su kasance karkashin sabon sashe na ma’aikatar.
Gwamnatin ta ce matakin na daga cikin manyan sauye-sauyen da take aiwatarwa a bangaren ilimi domin sake fasalta tsarin, kawar da maimaita ayyuka tsakanin ma’aikatu, inganta daidaiton manufofi a dukkan matakan ilimi, tare da rage kudin tafiyar da gwamnati.
Sakamakon haka, an umarci ofishin sakataren gwamnatin jihar da kuma ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati da su tabbatar da aiwatar da sauye-sauyen cikin gaggawa da kuma daidaita ma’aikatu da sassan da abin ya shafa.













































