Yarinya mai shekara takwas, Siyama Idris, ta rasu bayan ta fada bisa tsinin sandar karfen Rodi da aka bari a bude a wurin da ake aikin gyaran hanya da magudanar ruwa a unguwar Tudun Wada da ke karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wani ganau mai suna Abdulrashid Yusuf ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar a kusa da makarantar firamare ta Tudun Wada yayin da ake gudanar da aikin sake ginawa da fadada hanya tare da gina magudanan ruwa.
Yusuf ya ce an aika yarinyar ne wani shagon sayar da kayan masarufi da ke kusa domin ta sayo wani abu na buda baki lokacin da lamarin ya faru.
Ya kara da cewa magudanar ruwan da ake ginawa tana da sandunan karfe a bude, kuma babu wata hanyar ketarewa da aka tanada yadda ya kamata, lamarin da ya sa mazauna yankin ke amfani da gadar katako da aka yi na wucin gadi domin ketare magudanar.
Ya ce yayin da yarinyar ke kokarin ketare wurin da ake aikin, sai ta fadi bisa daya daga cikin sandunan karfen da aka kafa domin ginin magudanar ruwan kasancewar ba a rufe ta ba, kuma lokacin da ta fadi sai sandar ta soki cikinta, inda nan take ta rasu kafin a kai ta asibiti.
Mazauna yankin sun dora alhakin lamarin kan rashin tsauraran matakan tsaro a wurin aikin, suna cewa barin sandunan karfe a bude da kuma gefunan magudanan ruwa ba tare da kariya ba na jefa masu tafiya a kafa cikin hadari, musamman yara.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa barin karafe da sauran abubuwan da ke iya haddasa hadari a wuraren da ake aikin gina magudanan ruwa na kara zama ruwan dare a Kano, abin da ke janyo damuwa kan lafiyar jama’a.
Lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan wani matashi mai suna Ibrahim Umar mai kimanin shekara 15 ya fada cikin wata magudanar ruwa a kan titin Badawa da ke kusa da Lamido Crescent bayan sallar Juma’a.
Umar ya samu raunuka kuma dole ya sha ruwa kafin lokaci saboda an garzaya da shi wani asibiti da ke kusa domin yi masa magani.
Mazauna yankin sun bukaci hukumomi da kamfanonin da ke gudanar da ayyukan hanyoyi da magudanan ruwa da su tabbatar da daukar matakan tsaro da suka hada da rufe karafan da ke a bude tare da samar da hanyoyin ketarewa masu aminci domin kauce wa sake faruwar irin wannan mummunan lamari.













































