Sarkin musulmi na Sokoto ya kai wa shugaban kasa Tinubu ziyara

L R Sultan of Sokoto Alhaji Saad Abubakar and President Bola Tinubu 750x430

Shugaban kasa Bola Tinubu ya karbi bakuncin sarkin musulmi na Sokoto, Muhammadu Sa’adu Abubakar III, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Sarkin musulmin, wanda kuma shi ne shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya, ya kai ziyarar ne ga shugaban kasar a ranar Lahadi.

Sai dai har kawo lokacin hada wannan rahoto babu wani cikakken bayani kan abin da suka tattauna.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ziyarar na daga cikin jerin manyan ganawa da shugaban kasa Tinubu ke yi da fitattun shugabannin kasa da dattawan Najeriya a fadarsa.

A cikin kwanaki goma da suka gabata, shugaban kasar ya kuma karbi bakuncin dattijo kuma tsohon babban hafsan soja, Theophilus Yakubu Danjuma, da kuma tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon, a ziyarori daban-daban a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Gowon ya yi magana da ‘yan jarida bayan ganawarsa da shugaban kasar a ranar Asabar, inda ya yaba da yadda shugaban kasa Tinubu ke tafiyar da shugabanci.

Ya kara da cewa shugaban kasar na kokari wajen aiwatar da sauye-sauye da kuma inganta ci gaba a muhimman bangarori na tafiyar da harkokin gwamnati a Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here