Matatar man dangote ta rage farashin man fetur din ta zuwa kasa da Naira 900 kan kowace lita, domin samar da agajin da ‘yan Najeriya ke bukata kafin lokacin hutu.
SolaceBase ta rahoto cewa matatar mai ta farko mai zaman kanta a Afirka, wacce a baya ta rage farashin zuwa N970 ga kowace lita a ranar 24 ga Nuwamba, yanzu ta sanar da sabon farashin N899.50 kowace lita.
‘’Wannan ragi an yi shi ne domin saukaka farashin sufuri a lokacin bukukuwa, in ji sanarwar da babban jami’in kula da kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, ya fitar a ranar Alhamis.