Ruguzau: Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya Naira biliyan 8.5 

Abba Kabir Yusuf 1 750x430.jpeg

Babbar Kotun Jihar Kano ta umurci Gwamnatin Jihar Kano ta biya Lamash Properties Limited naira biliyan 8.511 a matsayin diyya kan rushe gine-ginen da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci a yi a watan Yuni 2023.

Haka kuma, an umarci gwamnan da lauyan gwamnati su biya karin naira miliyan 10 kudin shigar da kara.

Kotun, karkashin Mai Shari’a Sunusi Ma’aji, ta tabbatar da cewa Lamash Properties ta mallaki wuraren ta hanyar yarjejeniya ta doka tare da gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Ganduje.

Mai shari’ar ya bayyana rushewar a matsayin ba bisa ka’ida ba, kuma ya umurci a biya diyya saboda ba za a iya mayar da gine-ginen ba.

Wannan hukunci ya janyo wa gwamnatin jihar babban asara, biyo bayan matakan gwamna na rushe gine-gine da ya kira haramtattu, wanda ya ja cece-kuce tsakanin masu goyon baya da masu adawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here