Ziyarar Tinubu jihar Filato ba ta dace ba, rashin tausayi ce – Atiku

Atiku Abubakar1 650x430

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa halartar jana’iza a Jihar Filato maimakon ziyarar yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

Tinubu ya je Jos a ranar Asabar domin halartar jana’izar Mama Lydia Yilwatda, mahaifiyar shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.

A wajen bikin, shugaba Tinubu ya yi kira ga jama’a da su zauna lafiya tare da mutunta juna ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ba.

Labari mai alaƙa: “Ku daina haifar da rarrabuwar addini, matata fasto ce ni kuma Musulmi ne” – Tinubu ga ’yan Najeriya

Sai dai a wani saƙo da Atiku ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana ziyarar a matsayin “binciken fifiko marar daidai da kuma abin kunya ga shugabanci.”

Ya ce abin takaici ne ganin cewa shugaba Tinubu ya zabi halartar taron da ya shafi shugabansa na jam’iyya maimakon kai wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu ziyara a yankin Arewa ta Tsakiya..

Ya ƙara da cewa wannan halin na Tinubu yana nuna rashin tausayi da rashin jin zafin halin da jama’a ke ciki.

Atiku ya tunatar da cewa jihohin Benue, Neja da Kwara sun sha fama da hare-haren da ke kashe mutane, amma ba a taɓa ganin Shugaba Tinubu ya kai musu ziyara ba.

Ya kuma zargi shugaban ƙasar da guje wa yankunan da suka fi fuskantar matsalar ta’addanci a lokacin ziyararsa ta Benue a watan Yuni.

Atiku ya gargadi shugaba Tinubu da cewa ’yan Najeriya na lura da yadda yake tafiyar da harkokinsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here