Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ce ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika kan binciken da ake yi na wawure Naira 8,069,176,864.00.
Kamar yadda wani rahoto na musamman da jaridar Punch ta fitar, Sirika ya isa ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC da misalin karfe 1:00 na ranar Talata.
“A halin yanzu Sirika yana ganawa da jami’an hukumar EFCC domin amsa tambayoyi kan badakalar kwangilar da ake zarginsa da yi wa wani kamfani mai suna Engirios Nigeria Limited mallakin kanin sa Abubakar Sirika, inji jaridar.
“Yanzu haka yana ganawa da jami’an hukumar EFCC kan badakalar kwangilar kwangilar N8,069,176,864.00,” inji majiyar Punch.