A cikin jajircewa da karfin hali dangin wata amarya da gungun fasinjoji sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da su na kashe wani dan ta’adda a jihar Zamfara.
PRNigeria ta rawaito lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan ta’adda suka yiwa dangin amaryar da wasu matafiya kwanton bauna a hanyar Talata Mafara zuwa Gusau.
Karin labari: Kotu ta umarci EFCC ta gurfanar da lauyan Yahaya Bello
Dangin amaryar sun yi tafiya da nufin siyan tufafi da sauran kayan aure a jihar Kano. Duk da haka, shirin nasu ya ɗauki wani yanayi mai ban tsoro lokacin da ƴan fashi da makamin suka far musu.
Wani ganau ya bayyana cewa ‘yan fashin sun zabo wadanda abin ya shafa. Duk da daya daga cikin ‘yan fashin ya yi nasarar tserewa, sai dai acikin fasinjojin sun kama bindigu kirar AK-47 guda biyu.
Karin labari: Hukumar NAHCON ta kayyade wa’adin jerin alhazan jihohin bana
Jaridar PRNigeriya ta kara da cewa, a cikin jajircewar da tawagar ta yi, daya daga cikin fasinjojin ya samu bugun zuciya sakamakon abin da ya same shi, inda daga bisani ya rasu a asibiti.