
Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta umarci hukumomin jindadin Alhazai na jihohi da su kammala hada-hadar maniyyata zuwa rukuni na mutane 45 kowanne, da kuma shigar da bayanai zuwa yanar gizo na e-Track Portal, daga karshe zuwa ranar Juma’a.
A cewar hukumar, an ba da umarnin ne don tabbatar da samun saukin bayar da biza, da kuma bin umarnin hukumomin kasar Saudiyya da suka ba da umarnin hada mahajjata, inda ta kara da cewa za a ba da bizar ne kawai a lokacin da maniyyata suka kammala rukuni na 45.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Kotu a Kano ta sake ba da sabon umarni kan dakatar da Ganduje daga APC
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan yada labarai na NAHCON, Mousa Ubandawaki, a ranar Litinin.
A baya dai hukumar ta bayyana adadin maniyyatan da suka yi rajista a hukumance a matsayin maniyyata 51,477, wadanda suka kammala biyan kudin aikin Hajjin shekarar 2024, a karkashin kason gwamnati.
Karin labari: Shugaba Tinubu ya yi kira a samar da cibiyar yaki da ta’addanci a Afrika
Hakan ya biyo bayan maniyyata 48,414 da suka fara biyan kudin tafiya da aka sanar tun farko na Naira Miliyan 4.9, an bukaci su biya karin Naira Miliyan 1.9 sakamakon farashin kudin kasashen waje a halin yanzu.
A cikin sanarwar, Ubandawaki ya bukaci maniyyatan da ke son a hada su da su tunkari hukumomin jindadin su na jihohi daban-daban don tabbatar da cewa an yi musu rajista a rukuni guda 45, inda ya ce kungiyoyin za su gudanar da dukkan ayyukan Hajji tare da tafiye-tafiye da wurin kwana.
Karin labari: “Kashi 70 cikin 100 na fursunonin gidan yari a Kano na jiran shari’a” – NCoS
Haka kuma, ya kara da cewa NAHCON tana jan hankalin duk maniyyatan da ke son yin tafiya tare a rukunonin da ake bukata domin haduwa da hukumomin jindadin Alhazai na jiha domin a hada su da wadanda ake so.
Hukumar ta kuma yi nuni da cewa umarnin ya haifar da “dama ta karshe” da mahukuntan Saudiyya suka bayar na shirya tafiye-tafiyen rukuni na ayyukan Hajji.
Ya ci gaba da cewa bayan karewar wa’adin, alhazai za su kasance a tsare tare da zababbun mambobin kungiyar da biza za ta bayyana tare.












































