Kungiyar goyon bayan Tinubu ta kafa kwamitin yada labarai, dan jarida daga Kano ya shiga jerin sunaye

IMG 20260315 WA0283 750x430

An nada wani dan jarida da ke aiki a Kano, Ahmad Hamisu Gwale, a matsayin mamba a kwamitin yada labarai na kungiyar Tinubu Support Organisation, a wani mataki na karfafa tsarin sadarwa da yada ayyukan kungiyar ga jama’a.

Kungiyar ta sanar da jerin sunayen mambobin kwamitin ne a daidai lokacin da take shirin gudanar da wasu ayyuka, ciki har da shirye-shiryen gudanar da gasar kwallon kafa ta kasa domin gano hazikan matasa da kuma karfafa hadin kai ta hanyar wasanni.

Daraktan kula da harkokin kwallon kafa na kungiyar, Bashir Badawiy, ya bukaci mambobin kwamitin da su nuna jajircewa, kwarewa da kuma daukar nauyin da aka dora musu wajen yada shirye-shirye da manufofin kungiyar ga jama’a.

Badawiy ya bayyana bangaren yada labarai a matsayin muhimmin sashi na tsarin kungiyar, yana mai cewa yana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da isar da bayanai yadda ya kamata da kuma kyautata martabar kungiyar da ayyukanta a idon jama’a.

Ya kara da cewa an zabi mambobin kwamitin ne bisa la’akari da gogewarsu da kwarewarsu da kuma yadda za su iya sauke nauyin aikin da kungiyar ta dora musu.

Ya kuma bayyana cewa an zabo mambobin kwamitin daga dukkan yankuna shida na siyasar Najeriya.

Badawiy ya kuma bayyana cewa kwamitin zai kula da daidaita hulda da kafafen yada labarai, sarrafa kayan tallata ayyuka da kuma tabbatar da tattara bayanan dukkan shirye-shiryen kungiyar a fadin kasar.

Ya yabawa darakta-janar na aikin, Aminu Sulaiman, kan damar da aka bai wa mambobin kwamitin domin yin wannan hidima.

Za a gudanar da jagorancin kwamitin yada labaran ne tare tsakanin Jimoh Bashir da Eche Amos.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa sauran mambobin kwamitin sun hada da Andrew Randa, Attahiru Babayo, Ibitoye Shittu, Ayodeji Ismail, George Achigbe, David Jonathan Adebola, Oluchi Tobex, Solomon Onu, Igwe Solomon, Sunday Agunbiade, Olaiya Azeez da Sammy Wejinya.

Sauran sun hada da Kehinde Osagiede, Mr Frankie, Jackson Hananeel, Gaga Aliyu, Nasiru Kobi, Halilu Mohammed Telli, Nasiru Gide, Ahmad Hamisu Gwale, Jamilu Ubah, Ibrahim Tukur da Zakari Jibo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here