Kimanin ‘yan tawagar jihar Kano 21 da suke dawowa daga gasar wasannin motsa jiki ta kasa a jihar Ogun sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a karamar hukumar Kura.
SolaceBase ta ruwaito cewa motar dauke da mutane kusan 35 musamman ‘yan wasa da jami’ai, ta fado ne daga kan gada da misalin karfe 9:00 na safiyar yau Asabar wanda hakan ya yi sanadin wannan mummunan hatsarin.

Daya daga cikin tawagar, Ado Salisu, ya shaida wa SolaceBase cewa lamarin ya faru ne a dai-dai lokacin da tawagar ke daf da shigowa cikin birnin Kano bayan tafiyar dare da suka sha tun daga ranar Alhamis daga jihar Ogun, bayan kammala gasar wasanni ta kasa.
A yayin da aka sanar da mutuwar mutane 21, wasu da dama kuma sun samu raunuka kuma an garzaya da su babban asibitin garin Kura domin samun kulawar gaggawa.

SolaceBase ta kuma ruwaito cewa ana kokarin mika sauran wadanda suka samu raunika zuwa asibitin kwararru na Murtala da ke cikin birnin Kano.













































