Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, ta ce, adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a karamar hukumar Mokwa ya kai 151.
Mai magana da yawun hukumar, Ibrahim Hussaini ne ya bayyana hakan a safiyar yau Asabar.
Rahotonni sun bayyana cewa, mazauna yankuna uku da suka hada da Tiffin Maza da Anguwan Hausawa a karamar hukumar Mokwa sun nutse a daren ranar Laraba bayan da aka kwashe sa’o’i ana ruwan sama kamar da bakin kwarya.
Hussaini ya ce, mutane 11 sun samu raunuka yayin da 3,018 suka rasa matsugunansu.
Ya kara da cewa iftila’in ya shafi gidaje 265 da Kuma iyalai 503.
Lamarin dai na zuwa ne watanni biyar bayan da gwamnan jihar ta Niger Umar Bago ya bayyana cewa jihar ta karɓo bashin dala miliyan 10 daga bankin duniya domin magance zaizayar kasa a wasu yankunan Mokwa.
Gwamnan ya ce an gano kwararrun ‘yan kwangilar da za su gudanar da aikin.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da jami’an tsaro da su kara kaimi wajen ayyukan ceto da bayar da agaji a yankunan da lamarin ya shafa.











































