Gwamnatin tarayya na shirin kafa Kotun hukunta laifukan Jarrabawa

Tunji Alausa 750x430 (1)

Gwamnatin Tarayya ta ba da shawarar kafa wata Kotun Kotu hukunta ayyukan magudi da satar jarrabawa da za ta riƙa gaggawar wadanda aka samu da laifi domin daƙile cigaba da fuskantar matsalar a gaba.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana haka a Abuja yayin da yake karbar rahoton kwamitin inganta harkokin jarrabawa.

Da yake tabbatar da shawarwarin kwamitin mutum 17 karkashin jagorancin Farfesa Ishaq Oloyede, magatakardar hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ministan ya bayyana cewa hakan zai inganta fannin rubuta jarabawar a faɗin Najeriya.

Alausa ya tabbatar wa da ‘yan kwamitin cewa za a aiwatar da dukkan shawarwarin da suka bayar guda 12, inda ya ce gwamnati za ta tura dukkan na’urorinta domin yakar matsalar tabarbarewar jarrabawa.

“Bari na tabbatar wa dukkan ‘yan kwamitin cewa kun yi ayyukan da suka dace matuka, kuma duk shawarwarin da kuka ba mu a matsayinmu na gwamnati, za mu aiwatar da kowane daya daga cikinsu, in ji Ministan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here