Tawagar aikin ceto a yankunan da ibtila’in ambaliyar ruwa ta afku a garin Mokwa na jihar Neja ta ce zuwa yammacin yau Juma’a an gano gawar mutane 115 wadanda suka mutu.
Darakta Janar na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba Arah, ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ta hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ibrahim Hussain.
Abdullahi, ya ce sabanin alkaluman da suka gano sun tabbatar da samun gawarwakin mutane 115 da iftila’in ya, rutsa da su.
“Ya zuwa yanzu mun gano gawarwaki 115 kuma ana sa ran za a gano wasu da dama saboda ambaliya ta taso daga nesa tare da yin awo gaba da mutane da dama zuwa cikin kogin Niger, Kuma ana ci gaba da gano gawarqakin,” in ji Ibrahim Audu Husseini. “Don haka, adadin ke ci gaba da karuwa”.













































