Gwamna Yusuf ya ba da umarnin biyan albashin watan Maris kafin bikin karamar Sallah

WhatsApp Image 2025 11 14 at 20.52.54 1 750x430

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarnin a gaggauta sakin kudaden albashin watan Maris na shekarar 2026 tare da biyan su ga dukkan ma’aikatan gwamnati na jihar.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da daraktar wayar da kan jama’a a ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati, Rukayya Uba Sulaiman, ta fitar a ranar Asabar.

Sanarwar ta bayyana cewa mukaddashiyar shugabar ma’aikatan gwamnati, Haj. Bilkisu Shehu Maimota, ta ce an ba da wannan umarni ne domin bai wa ma’aikata damar shiryawa yadda ya kamata domin bikin karamar Sallah mai zuwa cikin sauki da mutunci.

Ta kara da cewa biyan albashin da wuri na nuna kudurin gwamnatin na kula da jin dadin ma’aikatan gwamnati tare da nuna godiya ga jajircewarsu da gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar.

Maimota ta kuma bukaci ma’aikatan gwamnati su yi amfani da wannan gata cikin hikima tare da ci gaba da nuna jajircewa, ladabi da kwarewa wajen gudanar da ayyukansu domin inganta hidimar gwamnati a jihar.

Ta kara da cewa gwamnatin jihar ta sake jaddada kudurinta na ci gaba da aiwatar da manufofi da za su inganta jin dadin ma’aikata tare da kara habaka yawan aiki a cikin ma’aikatar gwamnati.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here