An yi garkuwa da kwamishinan kasuwanci da farawa na jihar Bayelsa, Mista Otokito Federal Oparmiola.
An ce wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da Otokito a gidansa da ke Otukpoti a karamar hukumar Ogbia a daren jiya.
Daily Trust ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar yankin da ne da misalin karfe 11 na daren ranar Alhamis kuma bayan da suka tsorata mutane suka wuce gidan kwamishinan.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya ce yana cikin wani taro kuma zai sake kira.
Cikakkun bayanai daga baya…