A yau Juma’ar ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kasuwar zamani ta Sabon Gari da wasu ayyukan hanyoyi a kananan hukumomin Zariya da Sabon Gari na jihar Kaduna.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa Kasuwar Sabon Gari tana da shaguna 2,762, ginin ofishin gudanarwa na kasuwar wurin ajiye motoci, wajen ajiyar abinci, ofishin kashe gobara da ofishin jami’an tsaro da dai sauransu.
Shugaban ya kaddamar da kashi daya cikin biyu na ginin kasuwar, yayin da ba a kammala kashi na biyu dana uku ba.
Buhari tare da gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai da wasu ministoci, daga nan suka wuce fadar Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Bamalli, daga nan ya wuce Kaduna.
NAN ta ruwaito cewa Buhari ya je jihar Kaduna a ziyarar aiki ta kwanaki biyu bayan ya dawo daga Banjul na kasar Gambia, inda ya halarci bikin rantsar da shugaba Adama Barrow a karo na biyu a kan karagar mulki.
A lokacin da yake jihar, shugaban ya kaddamar da ayyuka a manyan garuruwa uku na Kaduna, Zaria da Kafanchan, wanda gwamnatin jihar ta aiwatar.
Jerin ayyukan sun hada da dandalin Murtala Muhammed da aka sake fasalinsa, asibitin masu fama da cututtuka, Dangote Peugeot Automobile Nigeria da Gadar Kawo Fly-over da dai sauransu.













































