Najeriya ta soki dogaro da makaman nukiliya, ta nemi a kawar da su gaba daya

Nuclear Weapon 750x430

Najeriya ta yi kira da a kawar da makaman nukiliya gaba ɗaya, tana mai gargadin cewa bil’adama ba za su iya ci gaba da dogaro da makaman da ke da ikon halaka fararan hula ba domin tabbatar da tsaron duniya baki ɗaya.

Wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, Amb. Jimoh Ibrahim, ne ya yi wannan kiran a ranar Talata a wani babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan kwance damarar makaman nukiliya da aka gudanar a New York.

An gudanar da taron ne domin tunawa da Ranar Kawar da Makaman Nukiliya Gaba Ɗaya ta Duniya, a yayin zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Jimoh ya ce Najeriya ta yi imanin cewa hanya ɗaya tilo da za ta ba da cikakken tabbaci kan hana amfani da makaman nukiliya ko barazanar amfani da su ita ce kawar da su gaba ɗaya.

Ya ce dubban makaman nukiliya har yanzu suna nan a duniya, yayin da ƙasashen da ke da irin waɗannan makamai ke ci gaba da sabunta su, a daidai lokacin da ake fama da ƙarin tashe-tashen hankulan siyasa tsakanin ƙasashe da matsin lamba kan tsarin kula da makamai na duniya.

“Najeriya ta yi imani da cewa hanya ɗaya tilo da za ta samar da cikakken tabbaci kan hana amfani da makaman nukiliya ko barazanar amfani da su ita ce kawar da su gaba ɗaya,” in ji Jimoh.

Jakadan ya ce Najeriya ba ta da makaman nukiliya kuma ba ta ɗauke su a matsayin wani abu da ya zama dole domin kare tsaron ƙasa ba.

“Najeriya ba ta mallaki makaman nukiliya, ba ta taɓa neman samar da shirin makaman nukiliya ba kuma ba ta da niyyar yin hakan. Tsaronmu bai dogara da makaman nukiliya ba,” in ji shi.

A cewarsa, ya kamata a gina tsaron duniya mai ɗorewa bisa tattaunawa, bin dokokin ƙasa da ƙasa, haɗin gwiwar ƙasashe da kuma tabbatar da tsaron dukkan ƙasashe ba tare da nuna bambanci ba.

Jimoh ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa ƙoƙarin duniya na samar da duniya marar makaman nukiliya.

“Shugaba Tinubu ya sha bayyana cewa Najeriya a shirye take ta yi aiki tare da ƙasashen duniya wajen inganta kwance damarar makaman nukiliya da hana yaɗuwarsu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa Najeriya na hangen duniya wadda babu wata ƙasa da ke buƙatar dogaro da makaman nukiliya domin kare tsaronta.

wakilin ya kuma yi kira ga ƙasashen da ke da makaman nukiliya da su cika wajibcinsu na kwance damarar makaman, kamar yadda Mataki na 6 na Yarjejeniyar Hana Yaɗuwar Makaman Nukiliya (NPT) ya tanada.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here