Tsohon Mukaddashin shugaban hukumar Yaki da cin hanci da rashawa EFCC, Ibrahim Magu, zai kammala aikin Dan Sanda a ranar 5 ga watan Mayun shekarar da muke ciki ta 2022, bayan ya cika shekaru 60 da haihuwa.
Magu ya fara aikin Dan Sanda ne tun a ranar 5 ga watan Maria na shekarar 1990 a matsayin mataimakin Sufuritanda, inda ya kai mukamin Kwamishina a ranar 18 ga watan Aprilun 201.
Rahotanni sun bayyana cewa tuni ya mika takardun nuna cewa ya lokacin yin ritayarsa ya kusanto ga hukumomin da abinda ya shafa.
Sai dai hukumar ‘Yan sanda ta Najeriya tace Kwamishinan ba zai samu hakkokinsa ba, har sai an Wanke shi daga zargin cin hanci da rashawa da yanzu haka Ministan Shari’a Abubakar Malami (SAN) ke tuhumarsa a kai.
Kwamishinan Yan sanda dake wakiltar mai magana da yawun hukumar kula da ayyuka da da’ar Yan sanda ta kasa, Mista Austin Braimoh, a ranar Asabar ya shaidawa jaridar PUNCH cewa Hukumar Yan sanda ba zata tattarawa Magu hakkokinsa na rutaya ba har sai an Wanke shi daga zarge-zargen da ake yi masa.
Tun a ranar 10 ga watan Yulin shekarar 2020 ne dai shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya dakatar da shi sakamakon zarge-zargen da Malami ke yi masa.













































