DA DUMI-DUMI: Buhari ya rattaba hannu kan dokar zartarwa ta 11 kan gyaran gine-ginen gwamnati

Buhari signs 1
Buhari signs 1

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan wata doka mai lamba 11 kan kula da gine-ginen gwamnati.

Rattaba hannu kan takardar ya biyo bayan taron mako-mako na majalisar zartarwa ta tarayya da aka gudanar a ranar Laraba a fadar shugaban kasa dake Abuja.

A jawabinsa jim kadan gabanin sanya hannun nasa, shugaba Buhari ya umurci dukkan ma’aikatu, da hukumomin gwamnati da su kafa sassan kula da gine-ginen, kamar yadda aka tanadar da sabuwar dokar zartarwa.

Shugaban ya jagoranci zaman majalisar wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha suka halarta.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folashade Yemi-Esan.

Ministocin da suka halarci taron sun hada da Lai Mohammed (Yada labarai da al’adu), Zainab Ahmed (Kasafin kudi, da kuma tsare-tsare na kasa), Babatunde Fashola (Ayyuka da gidaje), Ogbonnaya Onu (kimiyya da fasaha), Pauline Talen (ma’aikatar mata), da Suleiman Adamu. (albarkatun ruwa).

Haka kuma akwai Hadi Sirika (jirgin sama), Isa Pantami (communications and digital Economic), Chukwuemeka Nwajiuba (jihar ilimi), da Mohammed Abdullahi (kimiyya da fasaha), da dai sauransu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here