Dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin tutar jam’iyyar Labour Party, Bashir Bashir, ya kuma jam’iyyar APC.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar da ficewar dan takarar daga LP zuwa APC a yau Lahadi.
An tattaro rahotan cewa Malam Bashir ya gana da dan takarar shugabancin kasa a Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, tare da mataimakinsa Kashim Shettima, har sau biyu a jihar Lagos da Abuja, sannan sun yarda da sharadan da ya kafa na kumawar sa jam’iyyar APC.
Majiyar ta kara da cewa Malam Bashir ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu, sannan kuma yayi alkawarin mara masa baya dashi da magoya bayan sa a babban zabe mai zuwa.













































