Zaben 2023: Kungiyar kiristoci ta musanta karbar naira biliyan 2 daga hannun Peter Obi

Most Rev Daniel Okoh emerges CAN President.v1
Most Rev Daniel Okoh emerges CAN President.v1

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta ce bata da labarin cewa dantakara shugabacin kasa a Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya bawa cocinan dake karkashin kungiyar Naira biliyan biyu.

kamar yadda wata wasika mai dauke da sa hannun Pastor Frank Onwumere, take yawo a shafikan sada zumta, cewa Obi ya bawa cocinan Najeriya biliyan biyu, ta hannun CAN, domin su taimakeshi wajan tara masa mutanan da su zabe shi.

Shugaban kungiyar ta kasa, Daniel Okoh, ya karyata wasikar a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
“Hankalin shugabancin CAN, ya kai kan wata wasika dake yawo a shafikan sada zumunta, wacce ke cewa dantakarar shugabancin kasa a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya bawa cocinan Najeriya dake karashin CAN naira biliyan biyu.”
“Ina amfani da wannan dama na naisanta kungiyar CAN daga karbar wannan kudi, wannan wani yunkuri ne na saka CAN a cikin siyasa, CAN bata karbi kudin kowa ba.”

“Za kuma mu binciki tusah wasikar domin gano wanda ke da hannu wajan wanan karyar.”

“Ina so nayi amfani da wannan damar na shaidawa mutane cewa kungiyar CAN bata da alaka da siyasa, sanan kuma ba zata goyawa ko wane dan siyasa baya a zabe mai zuwa.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here