HOTUNA: Gwamnonin PDP suna gudanar da muhimmin taro a Rivers

WhatsApp Image 2022 01 17 at 2.28.14 PM 11
WhatsApp Image 2022 01 17 at 2.28.14 PM 11

Gwamnoni jam’iyyar PDP sun hallara a Fatakwal babban birnin jihar Rivers domin gudanar da wani muhimmin taro gabanin babban zabe na 2023.

Gwamnoni 10 ne suka isa wurin bikin dare da aka gudanar a dakin taro na Banquet dake gidan gwamnati.

Gwamnonin sun hada da Samuel Ortom (Benue) Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Seyi Makinde (Oyo), Okezie Ikpeazu (Abia) Bala Mohammed (Bauchi) da Umaru Fintiri (Adamawa) da mai masaukin baki, Nyesom Wike.

Sauran sun hada da Gwamna Aminu Tambuwal (Sokoto) Udom Emmanuel (Akwa Ibom), mataimakin jihar Zamfara, Mahdi Gusau, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, da sauran jami’an jam’iyyar na kasa.

Gwamnan Taraba, Darius Ishiaku, Sanata Ifeanyi Okowa (Delta), da Sanata Douye Diri (Bayelsa) sun isa wurin taron a ranar Litinin yayin da gwamnan Edo, Dokta Godwin Obaseki bai isa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here