Dakta Dauda Lawan-Dare ya sake lashe zaben fidda gwanin takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zamfara.
An sake zaben Lawan-Dare ne da kuri’u 422 a zaben fidda gwanin bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Gusau ta bada umarni.
Shugaban kwamitin zaben fidda gwanin gwamnan jam’iyyar ta PDP kuma shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna, Hassan Hyet ne ya bayyana haka a karshen taron da aka gudanar a Gusau.
Hyet, ya ce Lawan-Dare ya samu kuri’u 422 inda ya doke abokan takararsa su biyu wadanda suka samu kuri’u dai dai kowanne.
A cewarsa, daga cikin wakilai 431 da aka amince da su, 428 ne suka kada kuri’ar inda aka samu kuri’u hudu da ba su da inganci.
Ya ce Dakta Dada Lawan-Dare, ya samu kuri’u 422, Ibrahim Shehu da Hafiz Nuhuche suka samu kuri’u dai dai.
Tun da farko dai wata babbar kotu ce da ke Gusau, ta soke zaben fidda gwanin, a ranar 16 ga watan nan da muke ciki na Satumba.
A ranar 26 ga watan Mayun Shekarar nan ta 2022 ne dai Lawal-Dare, ya fito a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar.
Ya samu kuri’u 431 inda ya samu tikitin takara da Dakta Ibrahim Shehu wanda ya zo na biyu da kuri’u biyar yayin da Alhaji Wadatau Madawaki ya zo na uku da kuri’u uku.
A ranar 16 ga watan Satumba ne dai babbar kotun tarayya ta amince da koken ‘yan takarar da suka ki amincewa da sakamakon, tare da soke zaben fidda gwanin da aka yi, bisa rashin bin ka’ida acewar su.
Da yake yanke hukunci Mai shari’a Bappah-Aliyu, ya kuma nuna rashin amincewa da fitar da mata a cikin wakilan da suka halarci zaben na ranar 26 ga watan na Mayu.
Don haka ya ba da umarnin sake sabon zaben wanda dole ne ya kunshi wakilai akalla mace daya daga kowace gunduma cikin 147 na jihar.













































