Kamfanin sifirin jiragen saman Najeriya ya fara daukar Ma’aikata gabanin kaddamar da shi.

hadi sirika 1
hadi sirika 1

Kamfanin sifirin jiragen saman Najeriya wato Nigeria Air Ltd, sabon kamfanin jigilar kayayyaki na kasa ya fara daukar ma’aikata a manyan mukamai a kamfanin gabanin fara aiki.

Ma’aikatar sufurin jiragen saman Najeriya da ke karkashin Hadi Sirika ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a.

Dayake jawabi kan daukar ma’aikatan, Ministan Harkokin Jiragen Saman ya ce guraben da ake nema sun hadar da: “Kwararrun Kyaftin, ƙwararrun Jami’an masu daraja ta Daya dakuma ƙwararrun ma’aikatan jirgin, da gogaggun injiniyoyi.

“Kamfanin jirgin zai fara aiki nan bada jimawa ba da jirgin Boeing 737-800 (NG), sannan kuma jirgin B787 dazai rika aiki a cikin gida za a fara nan gaba kadan,” in ji Hadi.

Ya ce kamfanin zai fara da jiragen farko guda uku sannan kuma za a kara 30 a cikin shekaru biyu masu zuwa.

Kamfanin jirgin zai kaddamar da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin garjruwan Abuja da Legas amatakin farko yayin da sauran sifirin cikin gida za su biyo baya ba da jimawa ba, in ji ministan.

Sai dai ana sa ran majalisar zartaswa ta tarayya za ta amince da tsarin mallakar gidaje tsakanin makonni shida zuwa takwas.

Ma’aikatar ta ce hukumar NCC ta amince da shugabannin hukumar, kuma hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya ta bayar da izinin lasisin sufurin jiragen saman baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here