Majalisar wakilai ta yi sammacin Emefiele, tare da umarnin ya jingine tsarin kayyade cirar kudi

images
images

Majalisar wakilai ta bukaci babban bankin Najeriya da ya dakatar da shirin aiwatar da sabuwar manufar cire kudaden da aka shirya kaddamar wa ranar 9 ga watan Junairu badi har sai an cika sharuddan dokar da ta kafa bankin.

Haka zalika majalisar ta kuma gayyaci gwamnan babban bankin Godwin Emefiele kamar yadda dokar babban bankin ta tanada domin ya yiwa majalisar bayani kan manufofin bankin.

Zauren majalisar ya fusata a ranar Alhamis yayin da ‘yan majalisar ke yin Allah wadai da sabuwar manufar cire kudaden, suna masu cewa hakan zai yi matukar shafar kananan ‘yan kasuwa da tattalin arziki tunda akasarin al’ummomin karkara ba su da damar hada hada banki.

Sai dai kuma bayan wani batu da Mark Gbillah ya gabatar, Majalisar ta umurci Gwamnan CBN da ya gurfana gaban majalisar a ranar Alhamis 15 ga watan Disamba, 2022 domin yi wa majalisar bayani kan dalilin da ya sa ya dage kan takaita cirar adadin kudaden.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here