Najeriya ta fara binciken jami’an sojoji da ake zargi da shirin juyin mulki

Army keeps peace in Kaduna 680x430 (1)

Hukumomin sojojin Najeriya sun kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan wasu jami’an soja kusan ashirin da ake tsare da su bisa zargin shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa an kama jami’an sojoji goma sha shida a ƙarshen watan Satumba, ciki har da babban hafsan soja da wani kwamanda, bayan samun bayanan sirri cewa suna gudanar da tarurruka a asirce tare da nuna rashin gamsuwa da gwamnatin yanzu.

Wani jami’in soja ya tabbatar da cewa waɗanda aka kama suna shirin tsara juyin mulki mai zubar da jini, inda suka riga suka ware rana kafin shirin su fallasu.

Wannan labari ya jawo fargaba a gwamnati, inda hakan ya sa aka soke bikin ranar ’yancin kai da aka shirya gudanarwa a ranar ɗaya ga Oktoba, saboda tsoron wani abin da ka iya faruwa.

Rahotanni sun bayyana cewa an kafa kwamiti na musamman a rundunar sojoji domin binciken abin da aka bayyana da “rashim da’a da karya dokokin aiki”. Kodayake ba a bayyana cikakken sunayen mambobin kwamitin ba, majiyoyi sun ce akwai wakilai daga rundunonin soja, sojin sama, sojin ruwa, ’yan sanda da kuma hukumar tsaro ta farin kaya.

Duk da cewa rundunar tsaro ta ƙasa ba ta fito fili ta tabbatar da batun juyin mulkin ba, kakakin rundunar, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya bayyana cewa ana binciken jami’ai goma sha shida bisa laifin karya ƙa’idojin aiki da rashin da’a.

Wasu manyan jami’an soja sun ce binciken dai yana da alaƙa da zargin shirin kifar da gwamnatin Tinubu.

Majiyoyi sun ce an kama jami’an ne saboda tattaunawar da suka yi kan yiwuwar kifar da gwamnati, abin da ya zo daidai da lokacin da ake fama da ƙuncin tattalin arziki wanda ya sa wasu ’yan ƙasa suka rika kira da sojoji su karɓi mulki.

Hakan kuma ya biyo bayan juyin mulkin da ya faru a ƙasar Madagascar, wanda ya zama na tara a nahiyar Afirka tun daga shekara ta 2020.

Wani rahoto ya nuna cewa tunda aka gano wannan shiri, ba a sake gudanar da manyan bukukuwa na soji ba sai dai taron gaisuwar girmamawa a filin jirgi.

Ana tsare da jami’an da ake zargi a wani wuri na musamman da ba a bayyana ba a Abuja.

Bisa ga bayanin kakakin tsaro, bincike ya nuna cewa wasu daga cikin jami’an suna korafin tsaikon mukamai da rashin nasara a jarabawar karin girma.

Ya ƙara da cewa bayan kammala bincike, duk wanda aka tabbatar da laifi zai fuskanci hukunci da ya dace da tsarin rundunar soja domin tabbatar da adalci da kiyaye ƙwarewar aikin soja.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here