Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taron shugabanni na ƙasashen duniya da aka gudanar a birnin Rome na ƙasar Italiya, wanda aka shirya ƙarƙashin shirin Aqaba Process na ƙasar Jordan.
Shirin Aqaba Process wani tsarin haɗin gwiwa ne da Sarki Abdullah na biyu na Jordan ya ƙaddamar a shekarar 2015 domin yaƙi da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi.
Ana gudanar da shi ne ƙarƙashin jagorancin haɗin gwiwa tsakanin daular Hashemite ta Jordan da gwamnatin ƙasar Italiya.
Tinubu ya bar Najeriya a ranar 12 ga Oktoba domin halartar taron da aka fara gudanarwa a ranar 14 ga watan a Rome, inda ya jaddada kudirin Najeriya na ci gaba da haɗin kai da sauran ƙasashe wajen tabbatar da tsaro a yankin da ma duniya baki ɗaya.
Taron na wannan shekara ya mayar da hankali kan yadda kasashe za su ƙarfafa haɗin gwiwar yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi, musamman a yankin Yammacin Afirka.
Taron ya gudana a ranar Laraba, 15 ga Oktoba, a Gidan Tarihi na Fasaha ta Zamani da ta Gargajiya na Rome, tare da halartar shugabanni da dama ciki har da Sarki Abdullah na biyu na Jordan, Firayim Ministan Italiya Giorgia Meloni, da shugabannin ƙasashen Najeriya, Chadi, Paraguay, Saliyo da Togo.
Haka kuma, wasu manyan wakilai daga ƙasashen Aljeriya, Côte d’Ivoire, Kazakhstan, Mauritaniya, Senegal, da Uzbekistan sun halarci taron, inda aka gudanar da muhawara a sirri domin tsare-tsaren tsaro.
A gefen taron, Shugaba Tinubu ya yi ganawa da Firayim Ministan Italiya Giorgia Meloni da kuma mai ba da shawara ga tsohon shugaban Amurka Donald Trump kan harkokin Larabawa da Afirka, Massad Boulos.
Haka kuma ya gana da sakataren harkokin wajen Vatican, Kardinal Pietro Parolin, inda suka tattauna batun zaman lafiya da jituwa tsakanin addinai a Najeriya da kuma yadda za a magance ƙarya da ke yada cewa ƙasar ba ta da juriya ga bambancin addini.
Tun bayan kafuwarsa a 2015, Aqaba Process ya gudanar da taruka 33 a matakai daban-daban, daga na shugabanni zuwa na kwararru, tare da ginshiƙai uku da yake doruwa a kansu wato rigakafi, haɗin kai, da cike gibi a tsarin yaki da ta’addanci.












































