Kungiyar Alkhairi orphanage and women development (AOWD), ta roki gwamnatin jihar kano data amunce da bawa mata masu shayarwa hutun wata shida, domin su sami damar shayar da jariran su nono uwa zalla na tsawan wata shida.
Sanan kuma kungiyar ta kara neman da gwamnatain ta bawa iyaye maza suma hutun wata uku domin su sami damar taimakawa matayen su da suka haihu da wasu aikace aikace na gida.
Shugabar kungiyar, Hajiya Rukayya Abdurraham ce tai wannan kiran ranr Litinin a wajan wani taro da kungiyar ta shirya domin bakin murnar zagayowar makon shayar da jarirai nonon uwa zalla.
“Muna rokun gwamnati data taimaka ta amunce da bawa mata masu shayarwa hutu wata shida domin samun damar shayar da da jarirai yadda ya kamata.”
“Shayar da jarirar nonon uwa zalla abu ne mai kayu sosai, domin yana basu kariya daga kamuwa daga manyan cutittika ko da sun gairma.”













































