Sabon shugaban kamfanin NNPCL Ojulari ya karbi aiki daga hannun Kyari

L R Mele Kyari and Bashir 750x430

Sabon shugaban Kamfanin Mai na kasa NNPC Bayo Ojulari, ya karbi ragamar tafiyar da kamfanin daga hannun magabacinsa Mele Kyari.

Sanarwar da Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin na NNPC Olufemi Soneye, ya fitar ta bayyana cewa, mika aikin ya gudana ne a wani takaitaccen biki da aka yi a harabar NNPC ranar Juma’a a Abuja.

Ojulari ya yabawa Kyari bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen habaka kamfanin NNPC da kuma aikin da yake yiwa kasa.

Ya bayyana cewa makasudin gudanar da aikinsa shi ne karfafa nasarorin da magabata suka samar tare da kai kamfanin zuwa mataki na gaba.

Karanta: Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPCL

Ya ce, duk da cewa manufofin da aka sanya wa gudanarwar nasa suna da yawa, amma zai dogara ne da hadin kan mahukunta da ma’aikatan kamfanin, da kuma shawarar magabata don cimma burin da aka sanya a gaba.

Tun da farko a nasa jawabin, Kyari ya taya Ojulari murna tare da godewa mahukunta da ma’aikatan kamfanin bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake kan mukamin.

Ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don tallafa wa sabon shugaban don samun nasara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here