Shettima da Sauran makarraban gwamnatin tarayya sun hallarci taron rantsar da Okpebolo a matsayin Sabon Gwamnan Edo

Edo

A ranar Talata ne mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya wajen bikin rantsar da Sen. Monday Okpebolo a matsayin zababben gwamnan Edo na biyar bisa tafarkin dimokuradiyya.

Gwamna Shettima ya samu shiga tare da gwamnoni a fadin kasar, wadanda aka zaba a karkashin jam’iyyar (APC).

Gwamnonin APC sun hada da Sanwo-Olu na Legas, Dapo Abiodun na Ogun, Hope Uzodinma na Imo, da Ahmad Aliyu na Sokoto, da sauransu.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Umar Ganduje da kuma wanda ya gada, Sen. Adams Oshiomhole, suma sun halarci bikin, a filin wasa na Samuel Ogbemudia dake Benin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here