Mutum 13 sun rasa rayukansu a wajen hakar ma’adanan kasa a Plateau

images (10)
Aƙalla mutane 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon rushewar wani bigire a wajen hakar ma’adan kasa a Karamar Hukumar Bassa a Jihar Plateau, kamar yadda Dr. Joshua Riti, Shugaban Karamar Hukumar, ya tabbatar wa manema labarai a ranar Litinin a Jos.
Lamarin, wanda ya yi sanadin mutuwar matasa da dama, ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata.
Dr. Riti, wanda ya nuna bakin cikin sa game da mutuwar, ya ce mafi yawan wadanda suka rasu suna cikin shekaru 18 zuwa 30, kuma suna aiki ne don samun rufin asiri a cikin mawuyacin hali na tattalin arzikin ƙasar.
“Wannan wani lamari ne mai ban tausayi, wadannan matasan suna kokarin amfani da karfinsu don samun rayuwa da kuma tunkudar mawuyacin yanayin tattalin arziki a ƙasar, amma sai suka gamu da mutuwar da ba a zata ba,” in ji shi, yana mai mika ta’aziyya ga iyalan da suka rasa dangi.
Wurin rushewar ma’adinan, wanda ke kan iyakar Karamar Hukumar Bassa, Jos South, da Jos North, ya janyo hankalin duniya kan hadarin da ke fuskantar masu hakar ma’adanai a wannan yanki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here