Gwamnan Ribas Nyesom Wike yace idan har PDP ta cika jam’iyya ce me cikakken iko, to ta dakatar da shi daga jam’iyyar tareda jiran sakamakon abin da zai iya yi.
”Na ce idan sun isa su dakatar da ni a yau. Ba za su iya gwadawa ba saboda sun san abin da zan iya yi sakamakon hakan. Kuma duk yaron da ya hana mahaifiyarsa bacci, to itama tabbas baza ta rintsa ba kuma shi ma ba zai yi barcin ba,” inji shi.
Wike ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Fatakwal, inda ya ce jam’iyyar ta san abin da zai iya yi idan suka daddara suka dauki wannan mataki.
Gwamnan jihar Ribas ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu da yin kaka-gida a dukkan ayyukan jam’iyar, wanda hakan ke kara dagula rikicin jam’iyyar gabanin zabe.
Ya kuma ce duk da kiraye-kirayen da mabiyansa ke yi na cewa Ayu ya yi murabus ya kuma cika alkawarin da suka yi a baya na cewa tun da Atiku ya yi nasara zai yi murabus don share fagen samun daidaito da hada kai a jam’iyyar, Atiku da Ayu suka ki cika wannan alkawari da suka dauka.
Ya kara da cewa Atiku da Ayu da gaske ba su shirya lashe zaben 2023 ba, la’akari da irin rikicin da suka haifar.
Daganan Wike ya yi mamakin yadda jam’iyyar APC da PDP ke son tayar da ita ta ci gaba da tsare-tsare na shiyya-shiyya tare da mayar da matsayinsu na shugaban kasa zuwa yankin Kudancin Najeriya yayin da PDP tayiwa hakan bara’a.
Wike ya ce Prince Uche Secondus dan Kudu ne da aka cire shi a matsayin Shugaban jam’iyyar na kasa bisa yarjejeniyar da Gwamnonin Kudu suka yi cewa dan takarar Shugaban kasa ya fito daga Kudu, yayin da mukamin Shugaban kasa ya fito daga Arewa.
Ya bayyana hakan a matsayin abin takaici da rashin sanin ya kamata inda shugaban jam’iya, dan takarar shugaban kasa da Darakta Janar na yakin neman zaben shugaban kasa dukka suka fito daga Arewa.
“Ba zan ce Atiku da Ayu ba su da amana ba yanzu har sai munga abin da ya turewa buzu nadi, kasancewar ‘yan Najeriya ba su ji dadin mulkin gwamnatin APC ba”.













































