An sake samun rushewar gini a jihar Legas

FB IMG 1663934346457
FB IMG 1663934346457

An sake samun rushiwar gini a jihar Legas a kan titin Sonuga, layin Palm a unguwar Mushin.

Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, Dakta Olufemi Oke-Osanyinyolu, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma’a.

Ya ce, “Wani gini ya ruguje a Mushin ‘yan mintoci da suka wuce. Ana ci gaba da aikin ceto.”

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a iya tabbatar da cewa wani ya makale a cikin ɓaraguzan ginin da ya ruguje ɗin ba.

A cikin kwanakin nan jihar ta Legas na shan fama da rugujewar gine-gine da dama, lamarin da ya janyo asarar dukiya da kuma rayukan wasu mazauna garin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here