Mun Tallafawa Talakawa Sama Da Dubu 10 da Naman Sallah – Gidauniyar Niassé

FB IMG 1688159992445

Aminu bala madobi.

Gidauniyar kasa da kasa dake tallafawa gajiyayyu da mara sa karfi ta Niassé ta ce ta tallafawa gajiyayyu da marasa karfi sama da dubu 10 naman sallah anan Kano.

Shugaban Gidauniyar Sheikh Muhammad Abdul-ahad Ibrahim ne ya bayyana haka yayin gangamin rarraba naman sallar ga mabukata cikin tsarin Qurban2023.

Sheikh Abdul-ahad yace zasu cigaba da aiwatar da makamancin wannan tsari duk shekara domin rage radadi tareda sanya talakawa cikin jerin masu walwala.

Sheikh Abdul-ahad daganan ya bayyana jin dadi kan yadda wakilan gwamnatin kano suka basu cikakken goyon baya don samun nasarar shirin.

“Babu shakka mun sami nasarori da gagarumin cigaba cikin wannan tsarin a wannan shekarar” Sheikh Abdul-ahad.

Gidauniyar kasa da kasa ta Niasse da hadin gwiwar Kungiyar #Hasene Germany ne suka dauki nauyin wannan aiki ga mabukata a Najeriya.

Tun da farko dayake maida jawabi, Babban mai masaukin baki anan Kano, Alh. Sanusi Surajo kwankwaso ya godewa gidauniyar kan namijin kokarin ta na tallafawa dubun dubatar talakawa, masara karfi cikin alumma.

“Gaskiya naji dadi matuka yadda wannan Gidauniya tayi tsari mai kyau, ta rarrabawa talakawa jibga jibgan cinyoyin shanu don sanya su farin ciki” S.S Kwankwaso

Rahotanni sun ce a rana ta biyu an yanka Shanu Guda 750 aka raba a garin Rimin Gado dakuma wasu sassa ciki har da garin kwankwaso a karamar hukumar Madobi ta jihar Kano.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an kammala tsarin rarraba naman sallah ne a jihar jigawa wanda daga bisani suka dawo kano domin kai ziyara gidan marayu da zawarawa don sanya musu farin ciki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here