Shugaban jam’iyyar APC na jihar Ekiti, Paul Omotoso ya rasu.
Wata majiya ta bayyana cewa dan siyasar kuma lauyan haifaffen Imesi-Ekiti ya mutu ne da sanyin safiyar ranar Laraba bayan gajeriyar rashin lafiya.
Omotosho, wanda aka ce yana taka-tsantsan kuma ya halarci wasu tarurrukan siyasa a farkon makon, an ce ya koka kan rashin lafiyarsa a ranar Talata da ta sa aka garzaya da shi asibitin gwamnati da ke babban birnin jihar inda daga baya ya rasu.
Karin labari: Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano Ba Ta Da Ikon Binciken Bidiyon Dalar Ganduje – Kotu
Idan dai za’a iya tunawa a watan Yulin shekarar 2023 ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da marigayi shugaban jam’iyyar APC din, inda aka sake su bayan kwanaki biyar a cikin kogon ‘yan bindigar.
Mutuwar Omotoso ta biyo bayan rasuwar shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Ondo, Fatai Adams wanda ya rasu a tsakiyar watan Fabrairu.