Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano Ba Ta Da Ikon Binciken Bidiyon Dalar Ganduje – Kotu

Ganduja Smiling

Wata babar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ba ta da hurumin binciken shari’ar bidiyon dala na tsohon gwamna Abdullahi Ganduje.

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa alkalin kotun, Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman a ranar Talata ya yanke hukuncin cewa laifin yana karkashin dokar tarayya da hukumar jihar ba ta da iko a kai.

Idan dai za a iya tunawa, Abdullahi Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano ya maka hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano a gaban kotu inda ya bukaci alkalai da su dakatar da binciken da ya ke yi kan bidiyon na cin hancin dala.

Munan tafe da karin bayani

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here