Gwamnatin tarayya ta shiryawa ‘yan wasan Super Eagles maraba da tarba mai kyau a otal din Transcorp Hilton da ke babban birnin tarayyar Abuja.
Tawagar ta isa babban birnin kasar ne a daren Litinin din da ta gabata, biyo bayan rawar da suka taka a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON na shekarar 2024 a kasar Kwaddebuwa.
Super Eagles dai ta sha kashi da ci 2-1 a hannun mai masaukin baki a wasan karshe mai kayatarwa a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan a ranar Lahadi.
Karanta wannan: Super Eagles: Ahmed Musa da wasu sun yi kira a daina sukar dan wasa Iwobi
Taron maraba da karin kumallo ya samu halartar ministan matasa da wasanni John Enoh da shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF da sauran manyan baki.
Tawagar ‘yan wasa 25 na Super Eagles sun hada da manyan ‘yan wasa irin su Alex Iwobi da Ahmed Musa da Victor Osimhen da Ola Aina da Frank Onyeka da Calvin Bassey da Ademola Lookman da kuma Kenneth Omeruo da Joe Aribo tare da Williams Trost Ekong.