Fasinjoji sun lakadawa ma’aikatan jirgin sama duka a Legas

International Airline, fasinjoji, duka, ma'aikata, legas
Fasinjojin jirgin sama na Dana Airline sun lakadawa ma’aikatan kamfanin duka tare da lalata kayan aikinsu, saboda soke tashin jirginsu a filin jirgi na Muratala Mohammed da ke Legas. A yammacin ranar Litinin ne

Fasinjojin jirgin sama na Dana Airline sun lakadawa ma’aikatan kamfanin duka tare da lalata kayan aikinsu, saboda soke tashin jirginsu a filin jirgi na Murtala Mohammed da ke Legas.

A yammacin ranar Litinin ne fusatattun fasinjojin suka dauki matakin sakamakon tsaikon, inda suka lalata wurin da ake tantance fasinjoji kafin su hau jirgi.

Hatsaniyar ta barke ne bayan kamfanin jirgin ya sanar da soke tashin jirage biyu da za su Fatakwal da Owerri daga Legas da karfe 12 na rana, bayan fasinjojin sun shafe sa’o’i suna jira.

Karanta wannan: Super Eagles: Ahmed Musa da wasu sun yi kira a daina sukar dan wasa Iwobi

Majiyoyi a filin jirgin sun ce wasu fasinjojin sun makale a filin jirgin na sama da sa’o’i 24 bayan da aka dage tashin jirginsu da farko, daga karshe kuma aka soke.

Wani jami’i a filin jirgin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce “Wasu daga cikin fasinjojin tun jiya Lahadi suke jira bayan da aka dage tashin jirginsu.

An yi musu alkawari cewa jirginsu zai tashi yau Litinin amma bayan jinkirin da aka samu na sa’o’i uku, sai aka ce an soke tashin jirgin” Inji Jami’in.

Hakan ne ya sa fasinjojin fusata da kuma lalata na’urorin da kamfanin ke amfani da su a filin jirgin.

Karanta wannan: Super Eagles sun karbi tarba mai kyau bayan gasar cin kofin AFCON

Ma’aikatan filin jirgin sun ce a ranar Lahadi, kamfanin jirgin ya yi wa fasinjojin alkawarin cewa jirginsu zai tashi a ranar Litinin da karfe 10 na safe da 12 na rana, saboda matsalar da jirgin  ya samu.

“Abin takaicin sai kusan karfe 6 na yamma kamfanin jirgin saman Dana ya ba da sanarwar soke tashin jiragen biyu ba tare da wani jawabi mai gamsarwa ba, ko zaɓin maidowa jama’a kudadensu” A cewar wani ma’aikacin jirgin.

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Litinin a shafinsa na X, hukumar gudanarwar ta nemi afuwar fasinjojin saboda jinkirin da aka samu.

Daga karshe jami’an tsaron jiragen suka shiga lamarin inda aka kira fasinjojin jiragensu suka tashi da misalin karfe 9:00 na dare.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here