Matan gwamnonin Najeriya sun bukaci kafa dokar shan miyagun kwayoyi

Mata, Gwamnoni, Nigeria, doka, kwayoyi
Ganin yadda ake samun karuwar matasan dake rungumar mu'amala da miyagun kwayoyi, matan gwamnonin Najeriya sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da...

Ganin yadda ake samun karuwar matasan dake rungumar mu’amala da miyagun kwayoyi, matan gwamnonin Najeriya sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mazajen su da su kafa dokar ta baci domin dakile illar da kwayoyi ke yi a tsakanin al’umma.

Matan sun ce dokar ta bacin zata bada damar samar da kudaden da ake bukata domin tinkarar wannan matsala dake zama babbar barazana ga makomar matasan kasar nan.

Karanta wannan: Fasinjoji sun lakadawa ma’aikatan jirgin sama duka a Legas

Sanarwar da kakakin hukumar NDLEA Femi Babafemi ya gabatar tace, matan gwamnonin a karkashin jagorancin, Ambasada Olufolake Abdulrazaq, matar gwamnan jihar Kwara sun bukaci matakin ne bayan wani taron kwanaki 2 da suka yi da shugabannin hukumar NDLEA a kan illar da kwayoyin ke yi a fadin Najeriya.

Matan gwamnonin sun kuma bukaci inganta wuraren da aka tanada a jihohi domin kula da matasa da suka samu kan su a cikin halin amfani da kwayoyin dan ganin an dawo da su hanya.

Karanta wannan: ‘Yan kasuwa a Jihar Kano sun musanta zargin boye kayan abinci

Taron matan ya kuma bukaci sake duba matakan da ake dauka wajen yin tarbiya a tsakanin iyalai, wadanda suka ce ya yi rauni, inda suka bukaci iyaye su tashi tsaye wajen sauke nauyin dake kan su.

Sun yi alkawarin aiki tare da jami’an hukumar NDLEA da kuma sauran hukumomin tsaro wajen inganta hadin kan da ake bukata domin yaki da mu’amala da kwayoyin, yayin da kuma suka yi alkawarin bada gudunmawa wajen samar da akalla cibiyoyi 3 da za’a dinga taimakawa irin matasan da suka shiga irin wannan mummunar dabi’ar a kowacce mazabar ‘yan majalisun dattawa na jihohi.

Karanta wannan: Super Eagles sun karbi tarba mai kyau bayan gasar cin kofin AFCON

Matan sun yaba da irin matakan da shugaban hukumar NDLEA Janar Muhammadu Buba Marwa ke dauka na kara kaimin aikin jami’an sa na dakile safara da kuma shan kwayar a cikin kasa.

A karshe Janar Marwa ya yabawa matan gwamnonin saboda sha’awar da suka nuna na aiki tare da hukumarsa domin magance wannan matsala da kuma yadda suka jure halartar taron na kwanaki 2 lura da irin ayyukan dake gaban su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here