Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da babban aikin sake dubawa da inganta titin Kano–Kongolom da kudinsa ya kai Naira Biliyan 334.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Gwamna Yusuf ya bayyana amincewar da majalisar zartarwa ta tarayya FEC ta bayar a matsayin wani babban ci gaba na tarihi da zai sauya tsarin hanyoyin Kano tare da mayar da jihar cibiyar kasuwanci da harkokin sufuri a arewacin Najeriya.
Ya ce sabon tsarin aikin zai kai kilomita 132 kuma za a gina shi da hanyoyi uku na kankare tare da sanya fitilun tituna masu amfani da hasken rana da kuma na’urorin sa ido na CCTV na zamani.
Gwamnan ya ce hanyar Kano–Kongolom tana hada Kano da jihohin Jigawa da Katsina, wanda hakan ya sa ta kasance daya daga cikin muhimman hanyoyin tattalin arziki a yankin arewa maso yamma da kuma muhimmiyar kofar kasuwanci, noma da bunkasar masana’antu.
Gwamna Yusuf ya jaddada cewa girman jarin da aka saka a aikin yana nuna irin kudirin shugaban kasa Tinubu wajen bunkasa jihar Kano da ma daukacin yankin arewa maso yamma.
Ya kara da cewa aikin zai bude sabbin damar tattalin arziki ga manoma, ‘yan kasuwa da masu sufuri tare da rage lokacin tafiya da kuma inganta tsaro ga masu amfani da hanya.













































