Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhinin sa game da rasuwar tsohon kwamishinan kudi kuma malamin ilimi mai ƙwarewa, Farfesa Kabiru Isa Dandago.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanyawa hannu a ranar Laraba.
Gwamna Yusuf ya bayyana Farfesa Dandago a matsayin jajirtaccen jami’in gwamnati kuma kwararren masanin ilimi wanda gudummawarsa ga ilimi da shugabanci ta bar sawun da ba za a manta ba a Jihar Kano.
Ya lura cewa Farfesa Dandago ya yi wa jihar aiki da gaskiya da jajircewa, kuma mutane da dama sun girmama shi saboda kwarewa, saukin kai da kuma ƙaunar ilimi.
Gwamnan ya ce Jihar Kano ta rasa ɗan ta wanda gogewa da hikimarsa suka ƙara wa hidimar jama’a da al’umma ilimi sosai.
Gwamna Yusuf ya mika ta’aziyyarsa ta musamman ga iyalan marigayi, al’ummar malamai, da mutanen Jihar Kano bisa wannan babban rashi.
Ya yi addu’a ga Allah Mai girma ya gafarta wa marigayi Farfesa Isa Dandago, ya ba shi Aljannatul Firdaus, sannan ya ba iyalansa da masoyansa ƙarfin hali wajen jure wannan rashi.












































