Kotun tarayya da ke zama a Ibadan ta soke babban taron ƙasa na jam’iyyar PDP da aka gudanar a birnin Ibadan tsakanin ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba na shekarar 2025.
Alƙalin kotun, Uche Agomoh, ya kuma tabbatar da cewa kwamitin rikon ƙwarya na jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Mohammed Abdulrahman da Sanata Samuel Anyanwu shi ne kaɗai kwamitin gudanarwa na ƙasa da kotu ta amince da shi, har sai an gudanar da sahihin babban taron ƙasa.
Kotun ta tuna cewa ɓangaren jam’iyyar PDP ƙarƙashin Kabiru Turaki ne ya shigar da ƙarar mai lamba FHC/IB/CS/121/2025, inda suke neman amincewa da babban taron da aka yi a Ibadan a ranar 15 ga watan Nuwamba 2025 da kuma sahalewar kwamitin gudanarwa na ƙasa da ya fito daga taron.
Alƙali Uche Agomoh ya kuma hana Kabiru Turaki da sauran mutanen da aka zaɓa a wancan taro bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar PDP na ƙasa, tare da tabbatar da cewa taron an gudanar da shi ne ba tare da bin umarnin hukuncin kotu guda biyu da ke aiki ba.
Kotun ta bayyana cewa komawa neman sahalewar kotu bayan karya umarninta ba shi da wani amfani, don haka dukkan shawarwari da matakan da aka ɗauka a wancan babban taro kotu ta soke su baki ɗaya.
Bisa wannan hukunci, kotun ta ƙara jaddada cewa jam’iyyar PDP za ta ci gaba da aiki ne kawai ta hannun kwamitin rikon ƙwarya har sai an gudanar da ingantaccen babban taron ƙasa bisa doka.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, lauyan kwamitin rikon ƙwarya na PDP, Ferdinand Oshioke Orbih, ya bayyana hukuncin a matsayin wani ƙarfafawa ga dimokuraɗiyyar Najeriya, yana mai cewa kotun ta nuna cewa bin doka shi ne ya fi muhimmanci a kan muradin siyasa.
NAN













































