Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta haramta dukkan hawan Sallah Babba

Rundunar, 'yan sandan, jihar, Kano, haramta dukkan, hawan, sallah, babba
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Alhamis.Sanarwar tace...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar tace bayan karbar shawarwari, rundunar ‘yan sandan ta yanke hukuncin haramta dukkan wasu bukukuwan Sallah da ake gabatarwa na al’ada.

Idan dai ba’a manta ba da safiyar ranar ce babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta magantu kan dambarwar rikicin masarautar cewar tana da hurumin shiga shari’ar.

Karin labari: Babbar kotu a Abuja ta dage shari’ar Yahaya Bello

Hakan ce ta sa Mai shari’a MA Liman ya daga shari’ar zuwa ranar Juma’a 14 ga watan June 2024 domin ci gaba da shari’a.

Rigimar dai ta samo asali ne tun bayan da majalisar dokokin jihar da gwamnatin kano suka soke masarautun Kano tare da tsige Alhaji Aminu Ado Bayero daga masarautar da maye gurbin shi da Muhammadu Sanusi II.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here