Da dumi-dumi: Ganduje ya rushe ‘yan majalisar zartarwar sa.

Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje, ya baya da umarni ga dukkanin Kwamishinoni da shugabannin Ma’aikatu da hukumomin gwamnatin kano da su ajiye mukamansu nan da kwanaki Hudu masu zuwa

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babbar sakatariyar ofishin Bilkisu Shehu Maimota ta fitar, ta bukaci dukkan masu rike da mukaman dasu mika ofisoshin nan da kwanaki 4 daga yau.

Sanarwar ta kuma bukaci masu mukaman Siyasa da su mika ragamar ma’aikatunsu ga manyan Sakatarorin gwamnatin ko daraktoci ma’aikatunsu tare da kayan gwamnati dake wurinsu.

”Wadanda aka baiwa mukami yana da wa’adin sauka to su cigaba da rike mukamansu dai-dai da yadda dokokin suka tanadar”. A cewar sanarwar

Sanarwar daganan ta godewa daukacin wadanda suka rike mukaman bisa ga irin gudunmawar da suka baiwa gwamnati da kuma irin nasarorin da aka samu tsawon shekaru 8 da suka gabata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here